Yadda ta kaya a gasar kofin zakarun Turai

Champion League week 1
Bayanan hoto,

Karawar farko an ragargaza kwallaye a raga

Real Madrid ta yi ragargaza

Duk da rashin kokarin Real Madrid a gasar cin kofin La Ligar Spaniya, bai hana kungiyar lallasa FC Basel da ci 5-1 ba.

Fitattun 'yan wasan Madrid da suka hada da Gareth Bale da Cristiano Ronaldo da Karim Benzema da James Rodriguez ne suka zura kwallo a raga kowannensu.

Sai dai Atletico ba ta ji da dadi ba a hannun Olympiakos a gasar kofin zakarun Turai, inda aka doke ta 3-2 a Turkiya ranar Talata.

Liverpool sai ta zage damtse

Liverpool ta fara gasar cin kofin zakarun Turai da kafar dama, bayan da ta doke Ludogrets Razgrad da ci 2-1, duk da cewa rabonta da gasar shekaru biyar baya.

Da kyar Liverpool ta doke Ludogrets Razgrad wadda aka kafa a shekarar 2001, duk da cewa ta taba lashe kofin zakarun Turai karo biyar.

Arsenal na bukatar din ke bayanta

'Yan wasan Dortmund Ciro Immobile da Pierre-Emerick Aubameyang ne suka zura kwallaye biyu a ragar Arsenal.

Dortmund ta kai hare-hare da dama musammam dan kwallo Henrikh Mkhitaryan da ya zubar da damar maki da yawa.

Dortmund wadda ta taba lashe kofin a shekarar 1997, ta mamayi Arsenal da taka leda cikin salon gudu da tamaula tare da nuna gwaninta.

Manchester City ta kasa gano bakin zare

Har yanzu Manchester City ta kasa lakantar yadda ake buga gasar cin kofin zakarun Turai, ganin yadda ake hada ta da manyan kungiyoyi a rukuni

Duk da lashe kofin nan Premier Ingila guda biyu da kulob din yayi a cikin shekaru uku, har yanzu City ta kasa gano bakin zaren yadda za ta taka rawar gani a gasar.

Tsohon dan kwallon City Jerome Boateng ne ya zura kwallo tilo a raga, duk da cewa golan City Hart ya hana kwallaye da dama shiga raga a hare-haren da Munich ta dinga kaiwa.

An yi ruwan kwallaye a Rome da Portugal

Kulob din Roma na Italiya ya yi ruwan kwallaye 5-1 a ragar CSKA Moscow ta Rasha a rukunin da ya kunshi Bayern Munich da Manchester City.

Gervinho ne ya zura kwallaye biyu a raga, a inda mai tsaron bayan Brazil Maicon shima yana daga cikin wadanda suka zura kwallaye a raga.

Karawar da aka fi zazzaga kwallaye a raga shine wasan da FC Porto ta Portugal ta doke FC Bate da ci rabin dozin babu ko daya.

Dan kwallon Algeria Yacine Brahimi ya zura kwallaye uku a wasan.