Kofin Afirka: Masu karbar bakunci

CAF Logo
Bayanan hoto,

CAF za ta bayyana kasar da za ta karbi bakuncin gasar 2017

Hukumar kwallon kafar Afirka CAF ta zabi kasar Kamaru da Ivory Coast da Guinea su karbi bakuncin gasar cin kofin Nahiyar Afirka a taron da ta gabatar ranar Asabar.

A zaben da kwamitin amintattun hukumar kuri'ar ya kada a Ethiopia, ya amince Kamuru ta karbi bakunci gasar shekarar 2019, Ivory Coast ta karbi bakunci gasa ta 2021.

Haka kuma a wata sanarwar bazata CAF ta bayyana kasar Guinea a matsayin wadda za ta karbi bakuncin gasar cin kofin shekarar 2023.

Algeria da Zambia ba su sami izinin karbar bakunci ba, inda Jamhuriyar Congo ta janye daga takara tun watanni biyu baya.

Kenya da Algeria da Ethiopia da Ghana da Mali da kuma Zimbabwe na neman karbar bakuncin gasar kofin Nahiyar Afirka a shekarar 2017.

Libya ta janye daga karbar bakuncin gasar 2017, saboda rikicin da take fama da shi, kuma tuni CAF ta tsayar da karshen watan Satumba don mika takardar neman gasar 2017.

Za a bayyana kasar da za ta karbi bakuncin gasar cin kofin Nahiyar Afirka na shekarar ta 2017 a shekarar mai zuwa.