Kano Pillars ta doke Akwa United 1-0

Kano Pillars
Bayanan hoto,

Kano Pillars tana matsayi na daya a teburin Premier

Kulob din Kano Pillars ya doke Akwa United da ci daya mai ban haushi a gasar cin kofin Premier Nigeria wasannin mako na 27 da suka buga ranar Lahadi

Pillars ta samu maki uku ne ta hannun dan wasanta Adamu Hassan wanda ya zura kwallo a raga daf a tafi hutun rabin lokaci.

Sauran sakamakon wasanni da aka kara, Kaduna United tayi lagalaga da Crown Fc da ci ta 5-0, sai dolphins da ta doke Gombe 2-0.

Nasarawa United a garin Lafiya ta doke Sharks da ci 2-0, ita kuwa Enyimba ta casa Bayelsa United da kwallaye 4-0.

Har yanzu Kano Pillars tana matsayi na daya a teburi da maki 47, Nasarawa United na mataki na biyu da maki 44, sai Enyimba da maki 43 a matsayi na 3.

Ga sakamakon wasannin da aka buga ranar Lahadi:

Dolphin 2- 0 Gombe United El-Kanemi Warriors 2- 1 Heartland Enugu Rangers 1 - 0 Warri Wolves Enyimba FC 4- 0 Bayelsa United Giwa FC 3 - 0 Taraba FC Kaduna United 5- 0 Crown FC Kano Pillars 1 - 0 Akwa United Nasarawa United 2- 0 Sharks Sunshine Stars 3- 1 Abia Warriors