Leicester City ta doke Man United 5-3

Leicester Beat United
Bayanan hoto,

United tana matsayi na 13 a teburin Premier kenan

Kulob din Leicester City ya doke Manchester United da ci 5-3 a gasar cin kofin Premier Ingila wasan mako na biyar da suka kara a filin wasa na King Power.

United ce ta fara zura kwallo a raga ta hannun Robin van Persie, kafin daga baya Angel Di Maria ya kara kwallo ta biyu a raga.

Dan wasan Leicester Leonardo Ulloa ya rage kwallo da yaci da kai, sai dai kuma Ander Herrera ya kara wa United kwallo ta uku a raga.

Leicester City ta yunkuro ne yayinda David Nugent ya ci kwallo ta biyu a dukan fenarity, kuma Esteban Cambiasso ya farke kwallo ta uku wasa ya koma 3-3.

An zura wa United sauran kwallaye biyu ne ta hannun Jamie Vardy da kuma Ulloa wanda ya zura kwallaye biyu a wasa.