Man City da Chelsea sun tashi kunnen doki

Mancity Chelsea Draw
Bayanan hoto,

Har yanzu Chelsea tana matsayi na daya a teburin Premier

Manchester City da Chelsea sun tashi wasa kunnen doki a gasar cin kofin Premier Ingila wasannin mako na biyar da suka kara a filin wasa na Ettihad.

Chelsea ce ta fara zura kwallo a ragar City ta hannun dan kwallonta Andre Schurrle jim kadan bayan da aka bai wa Pablo Zabaleta jan kati.

Mai masaukin baki City ta farke kwallonta ta hannun tsohon dan wasan Chelsea Frank Lampard.

Lampard mai wasan tsakiya ya shiga karawar ne a sauyin dan kwallo, kuma ya samu damar farke kwallo da kungiyar da ya buga wa tamaula kimanin shekaru 13.

Chelsea har yanzu tana matsayi na daya a teburin Premier da maki 18, yayinda Manchester City ke mataki na 6 da maki 8.