An sa ranar zaben kujerar NFF

NFF Logo
Bayanan hoto,

Karshen watan Satumba za a gudanar da sabon zabe

Babban taron hukumar kwallon kafar Nigeria NFF karkashin jagorancin Aminu Maigari, ya tsayar da karshen watan Satumba domin gudanar da zaben sabbin shugabannin hukumar.

Taron da aka gudanar a Warri, jihar Delta ya kuma kafa kwamitin zabe da kuma kwamitin da zai karbi kararrakin zabe kamar yadda FIFA ta umarta.

'Yan takarar da suke neman shugabancin kujerar NFF, sun hada da Amanze Uchegbulam da Taiwo Ogunjobi da Mike Umeh da Dominic Iorfa da Shehu Dikko da Amaju Pinnick da kuma Abba Yola.

Jami'in yada labarai na NFF Ademola Olajire ya shaida wa BBC cewa taron ya amince da cewar mambobin da suka halarci babban taron hukumar na watan Nuwamba 2013 ne za su yi zaben bana.

Janar sakatare na NFF Musa Amadu ya ce an gudanar da babban taron hukumar kwallon kafar Nigeria ne ranar Asabar duk da rade-radin cewa kotu ta hana gabatar da taron.