Debuchy zai yi jinyar watanni uku

Mathieu Debuchy
Bayanan hoto,

Mathieu Debuchy zai yi jinyar watanni uku

Dan kwallon Arsenal Mathieu Debuchy, zai yi jinyar rauni na tsawon watanni uku, bayan da likitoci suka yi masa tiyata a kafarsa.

Debuchy, mai shekaru 29, sai sauya shi aka yi a karawar da suka yi da Manchester City, bayan ya fadi a birkice ranar 13 ga watan Satumba.

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce an samu nasarar yi wa dan kwallon tiyata, amma ya ji bakin cikin jin raunin dan wasan.

Wenger ya ce zai maye gurbin dan wasan da Calum Chambers, wanda ya dauko daga Southampton kan kudi fam miliyan 16 a watan Yuli.

Chambers mai shekaru 19 ya buga wa Arsenal karawar da ta doke Aston Villa da ci 3-0 har gida a ranar Asabar.