An ci zarafin Balotelli ta kafar Twitter

Mario Balotelli
Bayanan hoto,

'Yan sanda suna binciken wadanda suka ci zarafin dan wasan

'Yan sandan Birtaniya na binciken cin zarafin da aka aika wa dan kwallon Liverpool Mario Balotelli a dandalin sada zumunta na Twitter.

Dan wasan ya samu munanan sakwanni bayan da ya aike da sakon 'Man Unt...LOL lokacin da aka tashi wasan da Leicester ta doke Manchester United da ci 5-3 ranar Lahadi.

Sakon na Balotelli tamkar yana yi wa Manchester United dariya ne, saboda kashin da suka sha a hannun Leicester.

Balotelli mai shekaru 24 ya samu sakwanni fiye da 150,000 tare da munanan kalaman cin zarafi da kuma na wariyar launin fata.

Nan take dan kwallon ya goge sakon da ya rubuta da kuma dukkan cin mutuncin da aka aike masa.

'Yan sanda sun ce za su bibiyi wadanda suka maida martani ga Balotelli kuma daga ina suka aike sakon da kuma dalilan kalaman cin zarafin dana wariyar launin fata.

Balotelli, wanda ya buga karawar da West Ham ta doke Liverpool 3-1, ya sha fama da kalamun wariyar launin fata a karo da dama a baya.