CAF: Za a dage wa Gambia takunkumi

Gambia Football
Bayanan hoto,

CAF ta dakatar da Gambiya shiga harkar kwallon kafa tsawon shekaru biyu

Hukumar kwallon kafar Afirka CAF, ta ce za ta dage takunkumin da ta saka wa Gambiya, idan ta gamsu da zaben shugabannin kwallon kafar da aka yi an yi adalci a ranar Asabar.

An zabi tsohon kwamishinin wasannin kasar Modou Lamin Kabba Bajo, a matsayin sabon shugaban hukumar kwallon kafar ta Gambia a zaben.

A taron kwamitin amintattu da CAF ta gudanar a Ethiopia, ta amince da cewa za ta cire wa Gambia takunkumi idan ta gudanar da zaben shugabannin kwallon kafar kasar cikin adalci.

CAF ta dakatar da Gambia shiga harkar kwallon kafa, saboda samunta da laifin amfani da dan wasa da gangan wanda yake da takardun bogi da karyar shekarun haihuwa.

An gudanar da sabon zaben ne bayan da FIFA ta shiga tsakani a lokacin da aka sauke shugaban kwallon Gambia Mustapha Kebbeh a watan Yuli.