Qatar 2022: Allura za ta tono garma

FIFA Logo
Bayanan hoto,

An dade ana zargin mambobin FIFA da cin hanci

Rahoto kan zargin cin hanci da rashawa saboda bayar da izinin karbar bakuncin gasar kofin duniya a shekarar 2018 da 2022 zai iya shafar wasu daga cikin mambobin FIFA.

Wani lauyan Amurka Micheal Garcia ya kammala hada rahotansa kan zargin cin hancin da rashawa, sai dai kuma FIFA tace ba za a bayyana rahoton ga al'umma ba.

FIFA ta bai wa kasar Rasha izinin karbar bakuncin gasar cin kofin duniya na shekarar 2018 da kuma Qatar na shekarar 2018 a lokaci guda a shekarar 2010.

Mujallar Sunday Times ta zargi mataimakin shugaban FIFA Mohamed bin Hammam da bayar da toshiyar bakin fam miliyan uku, domin a bai wa Qatar bakuncin gasa.

Kwamitin karbar bakuncin gasar kofin duniya na kasar Qatar. ya karya ta dukkan zargin da aka yi masa.

Garcia ya yiwa sama da shaidu 75 tambayoyi kan zargin da ake yiwa mambobin FIFA, sannan kuma ya bada shawarwarin yadda ya kamata a dinga bi ana bada takarar karbar bakuncin gasar cin kofin duniya.