'Ronaldo ba ya bukatar hutun buga wasa'

Cristiano Ronald
Bayanan hoto,

Madrid tana bukatar Ronaldo domin yana kan ganiyarsa

Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya ce bashi da niyar bai wa Ronaldo hutun buga wa kulob din kwallo duk da buga wasanni hudu cikin kwanaki 12 da ya yi.

Ronaldo ya buga wa Madrid wasanni bakwai a bana, ciki har da gasar Super Cup ta nahiyar Turai da suka doke Sevilla da kuma wasanni biyu na gasar Super Cup din Spaniya.

Madrid za ta karbi bakuncin Elche a gasar cin kofin La Ligar Spaniya wasan mako na biyar ranar Talata.

Ancelotti ya ce Ronaldo baya bukatar hutu, domin yana kan ganiyarsa, kuma muna bukatar ya buga mana tamaula matuka.

Ronaldo mai shekaru 29 ya zura kwallaye shida a raga daga cikin wasanni hudu da ya buga baya, har da kwallaye uku rigis da ya zura wa Deportivo a karawar da suka doke su 8-2 ranar Asabar.

Madrid za ta ziyarci Villareal ranar Asabar a gasar cin kofin La Liga, kafin ta bakunci Ludogorets Razgrad ta Bulgeria a gasar cin kofin zakarun Turai ranar 1 ga watan Oktoba.