Walcott zai dawo tamaula a Oktoba

Theo Walcott
Bayanan hoto,

A Oktoba ake sa ran Theo Walcott zai dawo buga tamaula

Dan kwallon Ingila Theo Walcott na daf da dawowa buga wa Arsenal tamaula a watan Oktoba bayan kwashe watanni 10 da ya yi yana jinyar rauni.

Ana sa ran kila ya dawo buga wasa a lokacin da Ingila za ta kara da San Marino ranar 9 ga watan Oktoba da kuma Estonia kwanaki uku tsakani.

Walcott ya ji rauni a sawunsa na hagu a gasar cin kofin kalu-bale wato FA da suka kara da Tottenham a watan Janairu.

Idan Walcott ya dawo buga wasa a Oktoba, zai iya buga wa Ingila wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Turai da Slovenia ranar 15 ga watan Nuwamba, da kuma wasan sada zumunci da Scotland ranar 18 ga watan Nuwamba.

Tun farko an dibar wa dan wasan watanni shida zai yi jinya, daga baya likitoci suka ce raunin yana da girma da zai sa ya yi jinya mai tsawo kafin ya murmure.