Ghana Black Stars na farautar sabon koci

Ghana za ta kara da Guinea tar da kocin rikon kwarya
Kasar Ghana za ta kara da Guinea a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Afirka ba tare da kocin tawaagar 'yan kwallon kafar kasar ba.
Tsohon koci Kwesi Appiah ya raba gari da Ghana a farkon watan nan, kuma kasar ta rufe takardar zawarcin horas da kasar ranar 19 ga watan Satumba.
Wani mamba a kwamitin amintattun kungiyar kwallon kafar Ghana Fred Pappoe ya ce za su nada kocin rikon kwarya a karawar da za su yi da Guinea din.
Ghana za ta kara da Guinea a Morocco ranar 10 ga watan Satumba, kafin ta karbi bakuncin Guinea kwanki biyar tsakani.
Ana hasashen cewa tsohon kocin Ghana Milovan Rajevac ne zai maye gurbin Appiar a matsayin sabon kocin Black Stars.
Babban Labari
Minti Daya Da BBC
Saurari, MINTI ƊAYA DA BBC NA RANA 19/01/2021, Tsawon lokaci 1,04
MINTI ƊAYA DA BBC NA RANA 19/01/2021