An amince Liverpool ta fadada Anfield

Liverpool Anfield
Bayanan hoto,

A badi ake sa ran fadada filin wasa na Anfield

An amince Liverpool ta fadada filin wasanta na Anfield da ke cin 'yan kallo 45,000 zuwa 59,000 a cikin tsarin kashe fam miliyan 100 da kungiyar ta shirya kashewa.

Kwamitin tsare-tsare na birnin Liverpool ne ya amince wa kulob din kara babban sashen 'yan kallo da kujeru 8,300, da shiyyar titin Anfield da karin kujuru 'yan kallo 4,800.

Za a fara aikin fadada filin wasa na Anfield a badi, a kuma kammala ginin a shekarar 2016-17.

Sai dai masu adawa da aikin fadada filin sun yi korafin cewa kulob din ya so kansa wajen yin watsi da tarihin filin Anfield.

Samun damar fadada filin Anfield zai kara girman babbar farfadiyar 'yan kallon zuwa kashi uku, da gina dakin taro da wajen kayayyakin wasanni.