Kano Pillars za ta kara da Bayelsa United

Nigerian Premier League
Bayanan hoto,

za a buga wasannin mako na 28 ranar Laraba

Bayelsa United za ta karbi bakuncin Kano Pillars a gasar cin kofin Premier Nigeria wasannin mako na 28 da za su kara a birnin Benin ranar Laraba.

Sauran wasannin da za a kara sun hada da fafatawa tsakanin Sharks ta garin Fatakwal da Kaduna United, Lobi Stars ta karbi bakuncin Enyimba a garin Makurdi.

A jihar Abia za a kara ne tsakanin Abia Warriors da Enugu Rangers, sai Sunshine Stars da za ta ziyarci Taraba domin fafatawa da Taraba United.

Har yanzu Kano Pillars ce ke matsayi na daya a teburi da maki 47, bayan buga wasannin mako na 27, sai Nasarawa United a mataki na biyu da maki 44, inda Enyimba ke matsayi na uku da maki 43.

Ga jerin wasannin da za a kara ranar Laraba:

Abia Warriors vs Enugu Rangers Akwa United vs Giwa FC Bayelsa United vs Kano Pillars Crown FC vs El-Kanemi Warriors Gombe United vs Nasarawa United Heartland vs Nembe City FC Lobi Stars vs Enyimba FC Sharks vs Kaduna United Taraba FC vs Sunshine Stars Warri Wolves vs Dolphin