Saliyo na neman izinin buga wasa a Kamaru

Sierra Leone Team
Bayanan hoto,

CAF ta dakatar da buga wasanni a Saliyo saboda Ebola

Kasar Saliyo ta nemi izinin Kamaru da ta amince ta karbi bakuncin karawar da za su fafata a wasan neman tikitin shiga Gasar Kofin Nahiyar Afirka a Yaounde ranar 11 ga watan Oktoba.

Saliyo ta nemi izinin buga wasanta da Kamaru a Yaounde ne bayan da CAF ta saka wa kasar takunkumin buga tamaula a kasar don kaucewa kamuwa da cutar Ebola.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya a wani rahoto da ta fitar ranar 22 ga watan Satumba, kimanin mutane 2,800 suka mutu sakamakon cutar Ebola, kuma cikin wadanda suka mutu 560 'yan kasar Saliyo ne.

Idan Kamaru ta amince ta karbi bakuncin karawa da za suyi da Saliyo, hakan na nufin za su fafata sau biyu ke nan tsakanin kwanaki hudu.

Kamaru za ta karbi bakuncin Saliyo ranar 15 ga watan Satuma.