Asamoah Gyan ya musanta kashe abokinsa

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dan wasan ya zargi kafofin yada labaran Ghana da kokarin bata masa suna

Kyaftin din Ghana Asamoah Gyan ya ce zargin cewa ya kashe wani mawaki dan kasar, Castro da budurwarsa don yin tsafi, ba gaskiya ba ne.

Mawakin mai kidan Afro Castro, wanda sunansa na gaskiya Theophilus Tagoe, ya bata tare da budurwar Janet Bandu ne a watan Yuli.

Mutanen biyu sun bata ne lokacin da suka je yawon shakatawa da dan'uwan Asamoah Gyan a garin Ada na gabar tekun Ghana.

Kafofin yada labarai a Ghana sun yi zargin cewa lallai da walakin goro a miya.

An yi wa mawakin Castro da budurwar da suke tare, Janet Bandu ganin karshe lokacin da suke kan hanyar zuwa yawon shakatawa a teku, inda kuma ake tsammanin sun nutse a ruwa.

Ba a iya gano gawawwakin mamatan ba, yayin da aka ci gaba da yada jita-jita lokacin da dan'uwan Asamoah Gyan mai suna Baffour Gyan, da ake zargi yana da hannu a kashe mutanen biyu ya far wa wani dan jarida lokacin da yake tambayar dan wasan game da labarin da ake yadawa a gari.

A wani taron manema labarai, lauyan dan wasan mai shekaru 28, ya ce dangin Gyan suna matukar bakin ciki kan wannan batu, kuma sun yi shiru ne saboda kada su yi katsalandan a binciken 'yan sanda.