Routledge ya tsawaita kwantiragi a Swansea

Wayne Routledge Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya fi yin fice ne a kungiyar Swansea

Wayne Routledge ya tsawaita kwantiraginsa da Swansea na tsawon shekara guda, inda zai ci gaba da wasa da kulob din har zuwa karshen kakar 2018.

Routledge, tsohon dan kwallon Crystal Palace da Tottenham mai shekaru 29, ya koma Swansea City ne daga kungiyar Newcastle United cikin watan Agustan 2011.

Dan wasan ya buga wa Swansea wasannin Premier biyar a bana, ya kuma zura kwallo a karawar da suka doke West Bromwich Albion da ci 3-0 a watan Agusta.

Dan kwallon tawagar matasan Ingila 'yan kasa da shekaru 21, ya taka rawar gani a bara a Swansea, har ma ya zura kwallaye shida a raga.

Routledge, ya fara buga tamaula a Crystal Palace, ya kuma buga tamaula a kungiyoyi daban-daban guda tara, inda ya fi haskaka wa a kulob din Swansea City.