Platini: A wallafa rahoton cin hanci a Fifa

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Mai binciken ya ce ya zama wajibi ga kwamitin zartarwar Fifa ya ba da damar wallafa rahoton

Shugaban Uefa, Michael Platini ya ce ba zai yi adawa ga kiraye-kirayen a bayyana rahoton wani mai bincike, Michael Garcia kan zargin cin hanci a gasar kofin duniya ba.

A baya dai Fifa ta ce ba za a fitar da sakamakon binciken Michael Garcia game da tsarin neman gasar cin kofin duniya ta 2018 da ta 2022 ba, ko da yake, Ba'amurken mai binciken ya bukaci wallafa rahoton.

Michael Platini na daga cikin manyan jami'an Fifa na baya-bayan nan da suka mara baya ga bukatar Garcia ta samun tsare gaskiya.

Za a tattauna rahoton mai binciken a taron kwamitin zartarwar Fifa a yau.

Hakkin mallakar hoto Getty

An bai wa Rasha damar karbar bakuncin gasar cin kofin duniya ta 2018, aka zabi Qatar kuma don gasar shekara ta 2022.

Mataimakan shugaban Fifa, Jeffrey Webb da Yarima Ali bn Al-Hussein na Jordan da Jim Boyce su ma sun yi kira da fitar da muhimman bangarori da abun da rahoton ya gano.

Karin kiraye-kirayen wallafa rahoton ya biyo bayan bukatar da wani dan majalisar Burtaniya na jam'iyyar Consevative ya yi ga ofishin bincika manyan ayyukan almundaha na kwafen rahoton don kuwa yana iya janyo tuhume-tuhumen aikata manyan laifuka.

Kwamitin neman gasar cin kofin duniya na Qatar a 2022 na fuskantar zargin cin hanci bayan jaridar Sunday Times ta yi zargi a watan Yunin bana cewa tsohon mataimakin shugaban Fifa, Mohammed bn Hammam ya bai wa jami'an kwallon kafa na duniya fam miliyan uku don mara baya ga Qatar.