Messi ya zura kwallaye sama da 400 a raga

Lionel Messi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Messi ya ce bai taba tunanin zai ci kwallaye da yawa haka ba

Lionel Messi ya zura kwallonsa ta 401 a wasannin da ya buga wa Barcelona da Argentina jumulla a karawar da suka do ke Granada da ci 6-0 ranar Asabar.

Dan wasan Argentina mai shekaru 27, ya zura kwallonsa ta 400 da 401 a gasar La Liga wasan mako na shida da suka lashe Granada a Nou Camp.

Messi ya fara buga wa Barcelona wasa a shekarar 2004, ya zura kwallaye 359, ya zura 42 a Argentina cikin wasanni 506 da ya buga kafin karawa da Granada ranar Asabar.

Haka kuma ya lashe kyautar dan wasan da ya fi fice a duniya wato Ballon d'Or tsakanin 2009 zuwa 2012.

Dan wasan ya taimaka wa Barcelona lashe kofuna 21, ciki har da kofunan La Ligar Spaniya guda shida da kuma kofunan zakarun Turai uku.