Asia Games: An yi korafi kan 'yan Afirka

Maryam Yusuf Jamal Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Maryam 'yar kasar Baharain 'yar tseren meta 1,500

Ana ta korafi game da yadda 'yan asalin Afirka suke lashe kyaututtuka a Gasar Wasannin Asia, bayan da Maryam Yusuf Jamal ta kafa tarihi a tseren mata na mita 1,500.

Haifaffiyar kasar Habasha, wato Ethiopia, ta lashe zinare ne ta kuma kafa tarihi a tseren mita 1,500, daga baya 'yan kasar Morocco Mohamad Al-Garni da Rashid Ramzi suma suka lashe kyauta a matsayi na daya da na biyu na tseren maza.

Shi kuwa dan wasan Qatar Mutaz Aissa Barsham, bai karya tarihin da Javier Sotomaye ya kafa a duniya a wasan tsallen badake ba, amma ya lashe kyautar azurfa, kaninsa Muamer kuma ya lashe tagulla.

Mahukuntan Gasar sun yi korafi game da yadda 'yan asalin Afirka ke taka rawa a gasar, kwana daya bayan da dan wasan Nigeria, Femi Ogunode, ya doke 'yan wasan China da Japan ya kuma kafa tarihi a tseren mita 100 a Asia.

Sauran 'yan wasa a Gasar sun ce 'yan wasan na Afirka suna da tsawon da ya ke ba su damar tserewa abokan takara.

Su Bingtian, wanda ya lashe azurfa a tseren mita 100, ya ce "'Yan wasan suna da karfi da kuma kazar-kazar, a zahiri sun fi mu damar samun maki da dama".