Ibrahimovich ba zai buga wasa da Barca ba

Zlatan Ibrahimovic Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dan wasan yana fama da jinyar rauni a kafarsa ta hagu

Zlatan Ibrahimovic ba zai iya murmurewa kafin karawar da za su yi da tsohuwar kungiyarsa Barcelona a gasar cin kofin Zakarun Turai ranar Talata ba.

Kyaftin din Sweeden, mai shekaru 32, bai buga karawar da kulob dinsa PSG ya yi a gasar cin kofin Faransa ba sakamakon raunin da ya ji.

Likitocin kungiyar PSG sun yi masa gwaje-gwaje a kafarsa ta hagu da ta kumbura, inda suka ba da sakamakon cewar ba zai iya buga wasa ba a ranar Talata.

PSG ta buga kunnen doki da Ajax a wasan farko na cin kofin Zakarun Turai, a inda Barcelona ta doke Apoel Nicosia da ci daya mai ban haushi.

Dan kwallon Barcelona Andres Iniesta ka iya buga wa kulob din wasa na 100 a gasar kofin Zakarun Turai ranar Talata.