Giroud ya tsawaita kwantiragi da Arsenal

Olivier Giroud
Image caption Giroud yana daga cikin fitattun 'yan wasan Arsenal

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya sanar da cewa Olivier Giroud ya tsawaita kwantiraginsa da kulob din zuwa 2018.

Giroud, mai shekaru 28, ya koma Arsenal ne daga Montpellier a shekarar 2012kan kudi fam miliyan 12.

Dan kwallon bazai dawo buga tamaula ba, sakamakon raunin da ya ji har sai farkon shekarar badi.

Giroud ya ji rauni ne a karawar da Arsenal ta yi da Everton a wasan da suka tashi 2-2 cikin watan Agusta.