CAF ta dage wa Gambia takunkumi

Gambia Flag

Asalin hoton,

Bayanan hoto,

CAF ta dega wa Gambia takunkumi ne domin ta koma buga wasanni

Hukumar kwallon kafar Afirka CAF, ta janye wa Gambia takunkumin da ta saka mata na hanata shiga harkar kwallon kafa tsawon shekaru biyu.

Hakan ya biyo bayan da kasar ta gudanar da zaben shugaban hukumar kwallon kafar kasar, wanda tsohon ministan wasannin kasar Modou Lamin Kabba Bajo ya lashe zaben.

Kabba Bajo, mai shekaru 50, ya lashe zaben ne da kuri'u 28 daga cikin 51 da aka kada, inda abokin takararsa Buba Mbye Bojang ya samu kuri'u 23.

Kwamitin amintattun CAF ya amince da cire wa kasar takunkumi ne, bayan da ya tabbatar cewa an gudanar da zaben cikin walwala da adalci.

CAF ta dakatar da Gambiya shiga harkokin wasanni ne tsawon shekaru biyu, bayan da ta samu kasar da yin amfani da dan wasa da ya yi karyar a shekarun haihuwarsa.