Amanju Pinnick ne sabon shugaban NFF

Amaju Pinnick
Image caption Pinnick zai jagoranci NFF tsawon shekaru hudu

Amanju Pinnick ya lashe zaben shugaban hukumar kwallon kafar Nigeria wato NFF a zaben da aka gudanar ranar Talata a birnin Warri dake jihar Delta.

Pinnick mai shekaru 43, wanda shi ne kwamishinan wasannin jihar Delta, kuma shugaban kulob din Warri Wolves ya lashe zaben ne da kuri'u 32 daga cikin 44 da aka kada.

Abokin takararsa Dominic Iorfa ya samu kuri'u takwas, yayin da Taiwo Ogunjobi ya samu kuri'u hudu.

Shehu Dikko da aka yi hasashen zai iya lashe kujerar NFF janye wa ya yi daga takarar.

Yan takarar da suka yi zawarcin kujerar shugabancin NFF sun hada da Amanze Uchegbulam da Taiwo Ogunjobi da Mike Umeh da Dominic Iorfa da Shehu Dikko da Amaju Pinnick da kuma Abba Yola.

Gudanar da zaben NFF ya ceci Nigeria daga hukunta ta da Fifa tace za ta yi da ya hada da dakatar da ita shiga harkar kwallon kafa a duniya.