Padew zai iya jure matsi a Newcastle

Alan Padew Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin yana shan matsi daga magoya bayan kungiyar kan a kore shi

Alan Padew zai iya jure duk wani matsi da yake fuskanta sakamakon kwarewar da yake da ita a wasan kwallon kafa inji tsofaffin 'yan wasan kungiyar.

Newcastle tana matsayi na 19 a teburin Premier, bayan da magoya bayan kungiyar ke ta kiraye-kirayen a sallami kocin daga kulob din.

Shi ma tsohon dan kwallon Crystal Palace Mark Bright ya ce Padew daya ne daga cikin kociyoyin da ke jure matsi daga baya su kawo sakamako mai amfani.

Shekara ta biyar ke nan Padew yake horas da Newcastle, amma har yanzu kulob din bai lashe wasa a gasar bana ba.