NFF: Blatter ya goyi bayan zaben Pinnick

Amaju Pinnick
Image caption Ranar Laraba Pinnick zai fara kama aikin NFF

Shugaban hukumar kwallon kafa na Duniya Fifa Sepp Blatter ya goyi byan zaben da aka gudanar wanda ya dora Amanju Pinnick, a matsayin sabon shugaban kwallon kafar Nigeria wato NFF.

An zabi Pinnick, mai shekaru 43, kwamishinan wasanni kuma shugaban kwallon kafar jihar Delta sabon shugaban NFF ne ranar Talata.

A wasikar da Blatter ya rubuta wa Pinnick ya ce "Ina maka fatan alheri da samun kwarin gwiwa da nasarori, yayin gudanar da aikin da za ka kama, ina fatan za mu sadu nan bada dadewa ba".

Wannan jawabin ya kawar da shakkun cewa FIFA ka iya dakatar da Nigeria shiga harkar kwallon kafa a Duniya idan bata amince da zaben ba.

FIFA ta taba dakatar da Nigeria Shiga harkar kwallon kafa a watan Yuni, lokacin da aka sauke Aminu Maigari daga shugabancin hukumar NFF.