UEFA na binciken wasu kulob din Turai

football flares Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana samun yawan kunna hayaki a filayen wasa

Hukumar kwallon kafar Turai UEFA ta fara binciken kungiyar Galatasaray da Basel da kuma Borussia Dortmund, saboda tsaiko da magoya bayan kungiyoyin suka jawo a gasar cin kofin Zakarun Turai.

Arsenal ba za ta fuskanci hukunci mai tsauri ba, duk da kasa hana jefa hayaki mai tar-tsatsi cikin fili a karawar da suka doke Galatasaray 4-1 ranar Laraba.

A wasan Liverpool da Basel an jefi mataimakin alkalin wasa da batiri ne, yayinda magoya bayan Dortmund suka kunna hayakin da ya turnuke fili a Anderlecht.

Ranar 16 ga watan Oktoba ne hukumar kwallon kafar Turai za ta fidda hukuncin da za ta yiwa kungiyoyin.

Jami'an tsaro sun bada tabbacin cewa sun kama mutane shida a filin wasa na Emirates, biyu daga cikin su lokacin da suke kokarin shiga kallon wasan da abinda ke sa hayakin.