'Ruwan kwallaye muke so, Balotelli'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Brendan ya ce a matsayinsa na dan wasan gaba, sai ya sa kwazon cin kwallo ya kuma fito da hanyar cin kwallaye, amma Balotelli bai yi haka ba.

Kocin Liverpool, Brendan Rodgers ya fada wa dan wasan gaba na kungiyar, Mario Balotelli cewa sai kara zagewa wajen cin kwallaye sakamakon rashin tabuka wata kwakkwarar bajinta tun zuwansa Anfield.

Dan wasan na kasar Italiya mai shekaru 24, ya ci kwallo daya ne kacal a wasanni bakwai da ya buga tun bayan zuwansa Liverpool a kan fam miliyan 16 daga AC Milan.

Brendan Rodgers ya ce "Ta fuskar cin kwallaye, akwai bukatar ya kara himma, wannan ma ba sai an fada ba".

Ya ce ba ma kawai Balotelli ba, duk dan wasan gaba ana auna kwazonsa ne da yawan kwallaye, amma ya zuwa yanzu ga alama shi zazzaga kwallayen da ake tsammani ba.