Kluivert na cikin mutane 5 da ke son horas da Ghana

Partrick Kluivert Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana hasashen Kluivert ne zai zamo sabon kocin Ghana

Patrick Kluivert yana cikin jerin masu neman mukamin horas da Ghana su biyar da hukumar kwallon kafar kasar za ta fitar a nan gaba.

Ghana tana neman kocin da zai maye gurbin Kwesi Appiah wanda suka raba gari tun a watan Satumba.

Sauran wadanda suke zawarcin son horas da Ghana sun hada da tsohon kocin Chelsea Avram Grant da tsohon dan kwallon Italiya Marco Tardelli da dan kasar Sweeden Michel Pont da kuma dan kasar Spaniya Juan Ignacio Jimenez.

Hukumar kwallon kafar Ghana ta ce za ta gana da Pont da Kluivert da kuma Tardelli ranar 17 ga watan Oktoba, sannan ta gana da Grant da kuma Jimenez ranar 18 ga watan Oktoba.

Kluivert, tsohon dan kwallon Ajax da Barcelona, ya ajiye aikin mataimakin mai horas da Netherlands bayan kammala gasar cin kofin duniya a Brazil.