Kano Pillars ta doke Crown FC da ci 3-2

Kano Pillars Hakkin mallakar hoto kanopillarsweb
Image caption Saura wasanni 7 a kammala gasar Premier ta Nigeria

Kano Pillars ta samu nasara akan Crown FC da ci 3-2 a gasar kofin Premier ta Nigeria wasannin mako na 31 da suka kara ranar Laraba.

Sauran sakamakon wasanni da aka fafata su ne: kulob din Dolphins ya doke Kaduna United da ci 2-0, inda El-kanemi Warriors ta casa Nasarawa United da ci 3-1

Sharks ba ta ji da dadi ba a hannun Enyimba, inda aka zazzaga mata kwallaye 5-2 a garin Aba, Giwa FC ta doke Heartland da ci daya mai ban haushi.

Enugu Rangers ta samu maki uku rigis yayin da ta doke Bayelsa United da ci 2-1, Abia Warriors ta doke Taraba United da ci 2-0.

Sai a ranar Alhamis ne za a kara tsakanin Nembe City da Gombe United.

Har yanzu Kano Pillars tana matsayi na daya a teburin Premier da maki 53 bayan buga wasan mako na 31, Warri Wolves ta dare mataki na biyu da maki 49, yayin da Enyimba ke matsayi na uku da maki 48.

Ga sakamakon wasannin mako na 31 da aka buga ranar Laraba:

Abia Warriors 2 - 0 Taraba FC Dolphin 2 - 0 Kaduna United El-Kanemi Warriors 3 - 1 Nasarawa United Enugu Rangers 2 - 1 Bayelsa United Enyimba FC 5 - 2 Sharks Giwa FC 1 - 0 Heartland Kano Pillars 3 - 2 Crown FC Sunshine Stars 3 - 0 Lobi Stars Warri Wolves 2 - 0 Akwa United