Laurent Koscielny zai yi jinyar rauni

Laurent Koscielny Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption shi ma ya shiga cikin jerin 'yan kwallon Arsenal da ke yin jinya

Laurent Koscielny ya ji rauni a lokacin da yake atisaye da tawagar kwallon kafar Faransa, da hakan ya kara yawan 'yan wasa masu jinya a kulob din Arsenal.

Dan kwallon mai shekaru 29, ana sa ran zai samu sauki ya kuma buga wa Arsenal wasan Premier da za ta karbi bakuncin Hull City ranar 18 ga watan Oktoba.

Mesut Ozil zai yi jinyar tsawon watanni 10 zuwa 12, bayan da ya ji rauni a lokacin da yake atisaye da tawagar kwallon kafar Jamus ranar Laraba.

Tuni Aaron Ramsey da Mikel Arteta ba su buga wa Arsenal wasanni biyu ba sakamakon jinya da su ke yi.

Mathieu Debuchy da Olivier Giroud, sun dade suna yin jinya kuma da sauran watanni kafin su dawo buga tamaula.