Ingila ta lallasa San Marino da ci 5-0

Rooney vs San Marino Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ingila ta lashe wasanni biyu a jere, tana da maki shida

Ingila ta doke San Marino da ci 5-0 a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Turai da Faransa za ta karbi bakunci a 2016.

Phil Jagielka ne ya fara zura kwallo a ragar San Marino da kai, kafin daga baya Wayne Rooney ya zura kwallo ta biyu a dukan fenariti, kuma kwallonsa ta 42 da ya ciwa Ingila a wasa.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci Danny Welbeck ya kara kwallo ta uku a raga, wanda Andros Townsend ya kara kwallo ta hutu sai Alessandro Della Valle da ya ci kansu da kansa.

Nasarar da Ingila ta samu ya sa ta dare matsayi na daya a teburi da maki shida daga cikin rukuni na 5, bayan buga wasanni biyu.

Ga sakamakon wasannin da aka buga:

Belarus 0 - 2 Ukraine Macedonia 3 - 2 Luxembourg Slovakia 2 - 1 Spain England 5 - 0 San Marino Lithuania 1 - 0 Estonia Slovenia 1 - 0 Switzerland Liechtenstein 0 - 0 Montenegro Moldova 1 - 2 Austria Sweden 1 - 1 Russia