Ebola: Bangoura ba zai buga wa Guinea wasa ba

Alhassane Bangoura Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bangoura ya ce babu wanda ya tursasa shi kin buga wasan

Dan kwallon Guinea Alhassane Bangoura ya ce ba zai iya buga wa kasar wasa ba a karawar da za suyi da Ghana a wasan neman tikitin shiga kofin Afirka.

Bangoura ya ce ya yanke hakanne saboda abokan kwallonsa na kulob din Rayo Vallecano sun ce suna jin tsoron kar ya kamu da cutar Ebola.

Dubban jama'a ne suka mutu a Guinea sakamakon cutar Ebola, kuma tuni kasar ta mayar da wasanninta na neman tikitin shiga gasar Afirka zuwa Morocco.

Bangoura ya sanar ta shafin intanet na kulob din Rayo cewa da kanshi ya shaida wa kocin Guniea Michel Dussuyer cewa ba zai buga karawar da za su yi da Ghana ba.

Dan wasan ya ce kulob din Rayo Vallecano bai hana shi zuwa buga wasan ba, illa dai shi ne ya fuskanci abokan kwallonsa na fargabar kar ya je ya kamu da cutar Ebola.