Mensah ya ce har yanzu shi ne kocin Saliyo

Sierra Leone Team Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mensah ya ce yana da cikakkiyar kwarewar da ya kamata ya samu

Atto Mensah ya ce har yanzu shi ne kocin Saliyo duk da rade-radin da ake cewa John Ajina Sesay ne zai jagoranci kasar a karawa da Kamaru a wasan neman tikitin shiga kofin Afirka.

Hukumar kwallon kafar Saliyo ta ce Mensah ba shi da kwarewar da zai jagoranci kasar a karawar da za suyi da Kamaru.

Sai dai Mensah ya shaida wa BBC cewa yana da cikakkiyar kwarewar da zai iya jagorantar Saliyo ta samu tikitin shiga gasar kofin Afirka a badi.

Hukumar kwallon kafar Saliyo ce ta nada Mensah a matsayin sabon kocin tawagar kasar a watan Satumba, bayan da kasar ta raba gari da Johnny McKinstry.

Tuni hukumar kwallon kafar kasar ta umarci Sesay ya jagoranci tawagar sannan Abdulai Bah ya yi masa mataimaki a karawar da za suyi da Kamaru a Yaounde.