A Ingila ana nuna wariya miraran —Webb

Eddie Newton da Roberto Di Matteo Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jeffrey Webb ya ce an ki baiwa Eddie Newton (na gefen hagu) damar zaman koci

Shugaban kwamitin cika aiki kan wariyar launin fata na Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ya ce a fagen kwallon fakar Ingila baro-baro ake nuna wariyar launin fata.

Jeffrey Webb ya ce ba a boye wariya, sannan ya yi nuni da rashin bakar fata da tsirarun kabilu a cikin hukmomin gudanarwa na kungiyoyin kwallon kafa.

Shugaban Kungiyar Kwallon Kafa ta Kwararru a Ingila, Gordon Taylor, ya bayyana cewa nuna wariya boyayyiyar matsala ce.

Sai dai a cewar Webb, "Ba a boye take ba. An boye ta ne kawai daga jerin batutuwan da ake tattaunawa a kansu—ba wanda yake so ya fuskance ta".

Mista Webb, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban hukumar ta FIFA, kuma shugaban hukumar da ke kulla da kwallon kafa a yankin Caribbean, da Amurka, ya buga misali da kocin matasa na kungiyar Chelsea, Eddie Newton.

An ki a baiwa Newton, wanda ya yi aiki a matsayin mataimakin koci a karkashi Roberto di Matteo lokacin da Chelsea ta lashe Gasar Zakarun Turai a shekarar 2012, damar ganawa da shi don ya zama koci.

Karin bayani