Sharks ta doke Kano Pillars da ci 1-0

Kano Pillars Hakkin mallakar hoto Kano Pillars Web Site
Image caption Kano Pillars har yanzu tana matsayi na daya a teburi

Kungiyar kwallon kafa ta Sharks ta doke Kano Pillars da ci daya mai ban haushi a gasar Premier Nigeria wasan mako na 32 da su ka buga ranar Lahadi.

Sauran sakamakon wasanni da aka fafata Nasarawa United ta doke Nembe City da ci 3-2, yayin da Kaduna United da El-Kanemi su ka tashi wasa canjaras.

Warri Wolves har gida ta doke Bayelsa United da ci 2-1, Gombe United ma haka ta doke Enyimba ta Aba da ci 2-1.

Kungiyar Enugu Rangers kwallaye biyu ta kwasa a hannun Lobi Stars a Makurdi, karawa tsakanin Crown FC da Giwa FC su ka tashi wasa kunnen doki.

Har yanzu Kano Pillars ce ke matsayi na daya a teburi da maki 53, bayan buga wasannin mako na 31, sai Warri Wolves a mataki na biyu da maki 52.

Ga sakamakon wasannin da aka buga:

Akwa United 0 vs 0 Abia Warriors Bayelsa United 1 vs 2 Warri Wolves Crown FC 1 vs 1 Giwa FC Gombe United 2 vs 1 Enyimba FC Heartland 3 vs 0 Sunshine Stars Kaduna United 0 vs 0 El-Kanemi Warriors Lobi Stars 2 vs 0 Enugu Rangers Nasarawa United 3 vs 2 Nembe City FC Sharks 1 vs 0 Kano Pillars Taraba FC 2 vs 0 Dolphin