Walcott da Gnabry sun dawo Atisaye da Arsenal

Walcott and Gnabry Hakkin mallakar hoto arsenal
Image caption Arsenal na fama da 'yan wasan da suke jinyar rauni

Theo Walcott da Serge Gnabry sun dawo atisaye da kungiyar Arsenal da sanyin safiyar ranar Litinin bayan yin jinya da suka sha fama.

Walcott dan wasan Ingila rabonsa da buga tamaula tun karawar da kulob dinsa ya doke Tottenham da ci 2-0 a gasar kofin kalubale a watan Janairu.

Shi kuwa Serge Gnabry dan kwallon Jamus, rabon da ya buga wa Arsenal wasa tun a watan Maris sakamakon ciwon gwiwa da yake fama da shi.

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya kuma ce Olivier Giroud yana murmurewa cikin gaggawa, zai kuma dawo buga kwallo nan bada dadewa ba.

Giroud, mai shekaru 28 ya karye a kafarsa a karawar da suka tashi wasa 2-2 da Everton a wasan kofin Premier.

Arsenal tana matsayi na 8 a teburin Premier, za kuma ta karbi bakuncin Hull City a ranar Asabar, kafin ta ziyarci Anderlecht a wasan cin kofin zakarun Turai ranar 22 ga watan Oktoba.