AFCON 2015: Algeria na daf da samun tikiti

Sofiane Feghouli and Yacine Brahimi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Algeria ce ta daya a jerin kasashen da suka fi iya taka leda a Afirka

Algeria na daf da samun tikitin shiga gasar cin kofin Afirka da Morocco za ta karbi bakunci a badi idan ta doke Malawi a karawar da za su yi ranar Laraba.

Algeria wadda take matsayi na daya a jerin kasashen da suka fi iya taka leda a Afirka, ta lashe dukkan wasanni uku data buga a cikin rukuni na biyu.

Ana hasashen Algeria za ta doke Malawi ranar Laraba, sannan ta samu gurbin shiga gasar kofin Afirka a Morocco.

A karawar farko da su ka yi a Blantyre Algeria ce ta doke Malawi da ci 2-0, sannan za ta karbi bakuncin karawa ta biyu ranar Laraba.

Ga wasannin da za a buga ranar Laraba:

Cameroon v S Leone

Togo v Uganda

Cape Verde v M'bique

Angola v Lesotho

Ghana v Guinea

Nigeria v Sudan

Zambia v Niger

Egypt v Botswana

Ivory Coast v DR Congo

Burkina Faso v Gabon

Mali v Ethiopia

South Africa v Congo

Tunisia v Senegal

)Algeria v Malawi