Neymar ya zura wa Japan kwallaye hudu a raga

Neymar Brazil Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Brazil ta samu nasarar wasannin sada zumunci biyu data buga a jere

Brazil ta doke Japan da ci 4-0 a wasan sada zumunci da suka kara a Singapore, wanda Neyma ne ya zura dukkan kwallayen hudu a raga.

Neymar wanda yake buga tamaula a Barcelona mai shekaru 22, ya zura kwallaye 40 daga cikin wasanni 58 da ya buga wa Brazil.

Dan wasan ya fara zura kwallon farko a lokacin da ya tsinci tamaula cikin ribibi, ya kuma kara ta biyu daga kwallon da ya samu ta hannun Philippe Coutinho.

Neymar wanda ya taimakawa Brazil lashe Argentina da ci 2-0 ranar Asabar, ya kara kwallo ta uku da kuma ta hudu da kai a kwallon da Kaka ya bugo masa.

Dan kwallon Japan Shinji Okazaki ya kusan zura kwallo a ragar Brazil, a inda kwallon da ya buga da kafar dama ta bugi turke.