Jules Bianchi ba zai sare ba

Jules Bianchi a lokacin da aka kawo masa dauki da ya yi hadari Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Dan wasan tseren dai ya samu mummunan rauni akan sa a lokacin da yai hadarin.

Mahaifin dan wasan tseren mota Marussia Jules Bianchi ya ce ba su karaya ba duk da mummunan yanayin da yake ciki, bayan hadarin da ya yi.

Bafaranshen dan wasan mai shekaru 25 ya ji mummunan rauni a kansa, bayan taho mu gamar da suka yi da motar Suzuka ta daukar marasa lafiya.

Mahaifinsa Philippe Bianchi ya ce su na cikin wani yanayi mai wuyar fahimta, a duk lokacin da suka ji tarho ta yi kara su kan tsammaci ko daga asibiti ake son shaida musu Jules ya rasu.

Sai dai ya yi amanna da cewar dan na sa ba zai karaya ba, ya na da tabbacin idan ya farfado zai ci gaba da wasan tseren motar.

Haka kuma likitansa ya shaidawa Mahaifinsa cewa babu wanda ya taba yin irin wannan mummuna hadarin ya kuma tsira da ransa, dan haka ya na da tabbacin Jules ba zai sare ba.