'Ya dace van Gaal ya kara dauko 'yan wasa'

Di Maria and Falcao Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption United tana matsayi na hudu a teburin Premier

Tsohon kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya ce akwai bukatar United ta kara dauko fitattun 'yan kwallo.

Ferguson ya yi ritaya daga United a watan Mayun 2013, inda David Moyes ya maye gurbinsa, bayan watanni 10 kuma aka sallame shi daga aiki.

Van Gaal ya kashe sama da fam miliyan 150 wajen dauko sabbin 'yan wasa, ciki har da Angel Di Maria a matsayin dan wasa mafi tsada a Birtaniya.

Haka kuma United ta rabu da 'yan kwallo 14, ciki har da Danny Welbeck wanda ya koma Arsenal kan kudi fam miliyan 16.

Ferguson ya ce yakamata United ta kara dauko fitattun 'yan kwallo domin ta dawo da tagomashinta a fagen taka leda.