Ya kamata Fifa ta sauya tsarinta

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Fifa Sepp Blatter Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mr Garcia dai na sukar shugabancin sepp Blatter ne.

Shugaban sashen tabbatar da bin tsari an hukumar kwallon kafa ta Fifa Micheal Garcia ya bukaci hukumar da ta sauya tsarin yadda take gudanar da ayyukanta.

A wani jurwaye mai kamar wanka da aka yi wa shugabancin Sepp Blatter, Micheal Garcia ya ce ana bukatar a rika yin abubuwa cikin gaskiya da bin tsari ba tare da boye-boye ba.

Mr Garcia ya kara da cewa hukumar na bukatar shugabancin da zai samar da dokokin da za su shafi kowa-da-kowa.

Da yake jawabi akan binciken da ake yi a halin yanzu, Mr Garcia yace irin wannan tsari da ake amfani da shi ya fi dacewa ne a hukumomin bincike ko hukumomin leken asiri.

Amma ba tsari na wasanni na kasa da kasa ba, wanda manufarsa shi ne biyawa al'uma bukata wanda kuma al'umar na da hurumin bincikar abubuwan da ke wakana.