Suarez ya ci kwallon farko bayan kofin duniya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An dakatar da Suarez ne bayan ya ciji dan wasan Italiya a gasar cin kofin duniya

Tsohon dan wasan Liverpool Luis Suarez ya ci wa kasarsa ta Uruguay wasa a karon farko tun bayan gasar cin kofin duniya, lokacin da aka dakatar da shi da buga kwallo.

Dan wasan ya ci wasan ne a lokacin wasan sada zumunta da kasarsa ta fafata da Oman, inda ta lallasa su da ci 3-0.

Suarez, dan shekaru 27, yana ci gaba da yin biyayya ga dakatarwar da aka yi masa ta buga wasannin duniya na tsawo wata tara bayan cizon da ya yi wa dan wasan Italiya Giorgio Chiellini a gasar cin kofin duniya, kodayake zai iya buga wasannin sada zumunta.

A wasan da suka buga, Suarez ya ci kwallaye biyu dakikoki tara bayan dawowa daga hutun rabin lokacin, yayin da Jonathan Rodriguez ya zura kwallo ta uku.

Karin bayani