Nigeria ta yi wa Zambia kaca-kaca

Image caption Kyaftin din Nigeria kenan yayin taka leda a gasar zakarun Afirka

Nigeria ta lallasa Zambia da ci 6-0 don samun gurbi a zagayen kusa da na karshe a gasar zakarun Mata da ake karawa a Namibiya.

Zakarun na karo shida sun yi tafiyar ruwa da abokan karawarsu na rukunin A, inda Desire Oparanozie ta ci kwallaye biyu sai Ngozi Okobi da Osinachi Ohale da Asisat Oshoala da Perpetua Nkwocha suka jefa nasu kwallaye dai-dai kowacce.

Nigeria ta ci kwallon farko bayan minti biyu da sa wasa lokacin da Asisat Oshoala ta gara wa Okobi wata kwallo, ita kuma ta yi amfani da wannan damar.

Lamarin ya kara tabarbarewa Zambia lokacin da alkalin wasa ya kori 'yar wasan kungiyar Zulu bayan an ba ta katin gargadi a karo na biyu.

Wannan nasara ta bai wa Nigeria maki shida a wasannin da ta yi, inda take jagorantar rukunin, kuma a ranar Juma'a za ta fuskanci Namibia.