AFCON 2015: Morocco ta karyata kin karbar bakunci

afcon 2015 Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Cutar Ebola na kawo cikas a harkar kwallon Afirka

Ministan wasannin kasar Morocco ya karyata rahoton da ke cewa kasarsa ta fasa karbar bakuncin gasar cin kofin Nahiyar Afirka saboda tsoron yaduwar cutar Ebola.

Ministan kuma kakakin gwamnatin kasar Morocco, Mustapha Khalfi, ya ce har yanzu suna bukatar CAF ta gusar da gasar zuwa wani lokacin.

Hukumar kwallon kafar Afirka, CAF, ta ce ba za ta dage gasar daga lokacin da ta tsara buga kofin ba daga 17 ga watan Janairu zuwa 8 ga watan Fabrairu.

Tuni ma hukumar ta CAF ta tuntubi kasar Ghana da Afirka ta Kudu don jin ko akwai mai sha'awar karbar bakuncin gasar kamar yadda ta tsara.