Magoya bayan Arsenal za su yi gargadi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Magoya bayan Arsenal na son samun tabbaci daga wajen kungiyar

Magoya bayan kungiyar Arsenal za su gargadi kungiyar ta rage kudin kallon wasa bayan da wani rahoto da BBC ta wallafa ya nuna cewa kungiyar ce ta fi sayar da tikitin kallon wasa mafi tsada a gasar Premier.

Wani babban jami'in kungiyar, Stan Kroenke da sauran 'yan kwamitin zartarwarta za su fuskanci tambayoyi game da batun ranar Alhamis.

Kungiyar masu goyon bayan Arsenal tana so ta samu tabbaci daga jami'anta cewa ba za ta kara kudin sayar da tikiti a kakar wasa mai zuwa ba.

Ana sayar da tikitin kallon wasan kungiyar daga £97 zuwa £2,013.

Hakan ya nuna cewa farashin tiktin kungiyar ya ninka kusan sau bakwai kan kungiyoyi bakwai da ke fafatawa da kungiyar don darewa saman tebirin gasar Premier.

Karin bayani