CAF: Wa zai karbi bakuncin kofin Afirka

2015 Nations Cup Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Morocco tana fargabar kada a kai mata cutar Ebola

Hukumar kwallon kafar Afirka CAF ta yiwa Ghana da Afirka ta kudu tayin karbar bakuncin gasar cin kofin Nahiyar Afirka na badi.

CAF tana neman kasar da za ta karbi bakuncin kofin Afirka, sakamakon alamun dake nuna cewa Morocco na son janye wa daga karbar bakuncin wasan.

A makon da ya gabata Morocco ta bukaci CAF ta dage gasar kofin Afirkan zuwa wani lokaci, saboda tsoron kamuwa da kwayar cutar Ebola.

Bullar cutar Ebola a yammacin Afirka ya kawo koma baya a harkar kwallon kafar nahiyar, inda Saliyo ta dakatar da buga tamaula a kasar.

Haka kuma hukumar kwallon kafar Afirka CAF sai dakatar da taka leda a Guinea da Liberia da Saliyo.

Seychelles sai hakura ta yi da karawa da Saliyo a wasan neman tikitin shiga gasar kofin Afirka, saboda tsoron kamuwa da Ebola.