Kungiyoyin Turai na tsoron kamuwa da Ebola

Jurgen Klopp Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Cutar Ebola ta kawo koma baya a kwallon Afirka

Kocin Borussia Dortmund Jurgen Klopp ya ce kungiyoyin Turai na tsoron kamuwa da Ebola daga 'yan wasan Afirka masu zuwa buga wa kasarsu wasanni.

Klopp, na tararrabin yiwuwar buga gasar kofin Afirka a Morocco a Janairun badi, inda shugaban kulob din Lyon ya rubutawa FIFA hadarin dake tattare da buga gasar kofin Afirka saboda Ebola.

Wata kungiya a Spaniya ta hana dan wasan Guinea buga wa kasarsa wasan neman tikitin kofin Afirka, inda AC Milan ta karyata cewa Essien ya kamu da Ebola a karawar da ya buga wa Ghana tamaula a karshen mako.

Kimanin sama da mutane 4,500 ne suka mutu sakamakon cutar Ebola, inda Morocco ta bukaci CAF ta dage gasar zuwa wani lokaci.

CAF tace ba za ta dage gasar kamar yadda ta tsara yi daga 17 ga watan Januiru zuwa 8 ga watan Fabrairun badi ba.