NFF ta kori Stephen Keshi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An sha yin rade-radin cewa za a kori Keshi

Hukumar kwallon kafar Nigeria, NFF ta kori kocin Super Eagles Stephen Keshi daga aiki ranar Alhamis duk da doke Sudan da kungiyar ta yi da ci 3-1 a wasan da suka buga ranar Laraba.

A wata ganawar gaggawa da NFF ta yi, ta bayyana cewa ta nada tsohon kocin kungiyar Shuaibu Amodu a matsayin kocin rikon-kwarya.

Kazalika, NFF ta nada tsohon kocin Super Eagles Samson Siasia a matsayin mai horas da kungiyar 'yan kasa da shekaru 23.

Super Eagles dai ta koma baya a rukunin A da ke neman gurbi a gasar cin kofin nahiyar Africa da shekarar 2015 bayan da ta samu maki daya kacal a wasanni ukiu da ta buga, sai dai ci 3-1 da suka yi a wasansu da Sudan ya matsa da kungiyar zuwa matsayi na uku.

Da ma dai an yi ta rade-radin cewa za a kori Keshi, mai shekaru 52 a duniya, tun bayan gasar cin kofin kwallon kafar duniya da aka yi a Brazil a watan Yunin wannan shekarar.

Karin bayani